Shugaba Buhari Zai Tafi ƙasar Senegal Taron Harkokin Noma

 

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai tafi ƙasar Senegal ranar Talata domin halartar taron ƙasa da ƙasa kan harkokin noma karo na biyu da za a gudanar a birnin Dakar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ranar Litinin.

Taron wanda shugaban Senegal kuma shugaban ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU, Macky Salla zai karɓi baƙunci – an shirya shi ne domin samar da kyakkyawan yanayin noma domin ciyar da haniyar Afirka.

Mista Adesina ya ce maharta taron za su tattauna batun shigar da abinci da sauran kayan amfanin gona zuwa wasu ƙasashen, ciki har da Najeriya.

Ya ƙara da cewa yayin da nahiyar Afirka ke da mutum miliyan 249 da ke cikin ƙagin yunwa, taron – wanda shugabannin ƙasashen Afirka da ministocin kuɗaɗen da na noma na nahiyar, da ƙungiyoyin duniya za su halarta – zai saka aniyar kawar da yunwa a nahiyar Afirka nan da shekarar 2030.

Daga cikin tawagar da za ta yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa taron har da ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, da ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here