Shugaba Buhari ya ja Kunnen Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Tarayya da ke Tattara Haraji

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan kasafin kudin sabuwar shekarar 2021.

A jawabin da ya gabatar yayin saka hannu a kan kasafin kudin, shugaba Buhari ya ja kunnen hukumomi da ma’aikatun da ke tattara haraji.

Buhari ya ce zai dauki mataki tare da saka takunkumi akan shugabannin hukumomi da ma’aikatun da suka gaza sauke nayinsu.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ja kunnen ma’aikatu da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da ke tattara haraji da su tashi tsaye don ganin sun samar da isassun kuɗaɗen shiga.

Mataimakiyar shugaba ta musamman kan shafukan sadarwa ga shugaba Buhari, Lauretta Onochie, ce ta bayyana cewa, shugaban ya fitar da wannan gargadin ne yau 31 ga watan Disambar lokacin da ya ke rattaba hannu kan kasafin kudin shekara 2021 mai kamawa.

Bayan sa hannu a kasafin na kimanin tiriliyan ₦13.588 wanda ya zama doka, shugaban ya ce, “Muna rubanya kokarinmu don tabbatar da mun samu isassun kuɗaɗe na kasafin 2021.

“Wajibi ne ga hukumomi su tabbatar da burinmu na samar da danyen mai da fitar da shi ƙasashen waje.

“Duk shugaban da ya yi sakaci wajen sauke hakkinsa za mu ɗauki mataki mai tsauri kansa. Ina kira ga yan ƙasa da su yi ƙoƙarin biyan haraji kan lokaci,” a cewar Buhari.

Buhari ya kara da cewa, “Duk da annobar COVID-19, mun yi manyan aiyuka da abubuwan da ya kamata a yaba daga kasafin kudin shekarar 2020”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here