Shugaba Buhari ya Jagoranci Taron Tsaro a Fadar Gwamnati da ke Abuja
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron tsaro a fadar gwamnati da ke birnin tarayya Abuja yau Alhamis.
Manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan na Sojojin ƙasa, sama da ruwa, Sufetan yan sanda da sauran su duk sun samu halartar taron.
Taron na zuwa ne a dai-dai lokacin tsaro a Najeriya ke ƙara taɓarɓarewa musamman a arewacin ƙasar.
Abuja – Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron majalisar koli ta tsaro a fadar gwamnati da ke babban birnin tarayya Abuja, ranar Alhamis.
Buhari, Sallau, babban mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin kafafen sada zumunta ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar haɗe da Hotuna a shafinsa na Tuwita.
Read Also:
“Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron tsaro a gidan gwamnati ranar 21 ga watan Yuli, 2022,” inji sanarwan.
Taron ya samu halartar Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, da kuma mai ba da shawar kan harkokin tsaro na ƙasa, Babagana Monguno.
Babban Hafsan tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor, shugaban sojin ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo da shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao, duk sun halarci taron.
Sauran mahalarta taron sun haɗa da, Sufeta Janar na yan sanda, Usman Alƙali Baba, Darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, da kuma daraktar hukumar tsaron fasaha, (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.