‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Yankin Jihar Neja

Rahoto daga majiya mai tushe ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka farmaki wani kauye a yankin jihar Neja.

An ga mazauna yankin da lamarin ya shafa suna gudun tsira, tare da boye shanunsu daga sacewar ‘yan bindiga.

Ana yawan samun hare-hare a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin da ya raba jama’a da gidajensu.

Kontagora, jihar Neja – A safiyar yau Alhamis ne ‘yan ta’adda suka mamaye wasu al’ummomin yankin Kamapani Waya a karamar hukumar Kontagora a jihar Neja.

Wakilin The Nation, wanda ke kan hanyar zuwa Kontagora daga Minna a motar haya, ya koma da baya bayan ya bar yankin Kampani Waya.

Wasu motoci ne suka sanar da direban motar cewa, akwai ‘yan bindiga da ke barna kan mutanen kauyen.

Rahoton jaridar ya ce, mutanen da ke motar sai da suka koma Kampani Waya kana suka zauna a can na kusan mintuna 40.

An ga mutanen kauyen cikin shiri yayin da wasu ke kira ga mata da yara su je su buya. Hakazalika, wasu sun kwashe shanunsu domin boyesu.

Duk motocin da suka taho daga Minna sai da suka tsaya don gudun shiga cikin tashin hankalin da ‘yan bindigan ka iya jefa su.

A bangare guda, jaridar ta yada bidiyon lokacin da motoci ke barin hanyar bayan samun labarin ‘yadda ‘yan ta’addan ke barna a yankin na jihar Neja.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here