Shugaba Buhari ya Jajantawa Waɗanda Harin Boko Haram ya Shafa a Adamawa

 

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jajantawa waɗanda harin da mayaƙan Boko Haram ya shafa a jahar Adamawa.

Yan ta’addan sun kai hari ne a gariɓ Kwapre ranar jumu’a 9 ga watan Afrilu, inda suka yi ma mutanen yankin mummunan ɓanna.

Shugaba Buhari, wanda sakatarensa Boss Mustapha ya wakilta yace gwamnati zata kawo ɗauki, kuma za’a ɗau matakan kiyaye hakan nan gaba Shugaba Buhari yayi ta’aziyya ga mutanen yankin Kwapre dake ƙaramar hukumar Hong, jahar Adamawa bisa harin da mayaƙan Boko Haram suka kai musu kwanan nan.

Shugaban wanda sakataren gwamnatinsa, Boss Mustapha ya wakilta, ya bayyana haƙa ne a wata ziyara da yakai yankin da abun yafaru, Vanguard ta ruwaito.

Boss Mustapha yace: “Nazo Kwapre ne inga abinda ya faru bisa umarnin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, shugaban yana muku jaje da ta’aziyyar lamarin da ya faru.”

“Nagani da idona irin ɓarnar da aka yi muku, nayi matuƙar baƙin cikin ganin ɓarnar, amma ina mai tabbatar muku gwamnatin tarayya zata yi duk abinda ya dace wajen kare rayuwar mutane da dukiyoyinsu.”

Sakataren ya ƙara da cewa a bayanan da ya samu an lalata gidaje sama da 78, shaguna 12, makarantu da kuma wuraren Ibada guda huɗu.

Ya ce kare rayuwar al’umma aiki ne na mutane da dama bawai gwamnati kaɗai ba, mutanen dake rayuwa a wajen suna da babbar rawar da zasu taka.

Daga ƙarshe sakataren gwamnatin ya ce FG zata ɗauki duk matakan da ya dace wajen ganin haƙan bai sake faruwa ba. Kuma zata taimaka wajen gyara wuraraen da aka lalata.

Manajan ma’aikatar jinkai ta yanmin arewa maso gabas, Mr Musa Zarami, yace hukumar su t samar da kayayyakin jinkai ga waɗanda abun ya shafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here