Yawaitar Hare-Hare: Ba Zai Yiwu Shugaba Buhari ya Je Jaje ko ina ba – Maigari Dingyadi
Ministan da ke lura da harkokin ‘yan sandan Najeriya Maigari Dingyadi ya ce ba zai yiwu shugaban kasar Muhammadu Buhari ya je jaje ko ina ba saboda yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a kasar
Ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa a daidai lokacin da ‘yan kasar suke ci gaba da caccakar Shugaba Buhari bisa rashin zuwa jihar Sokoto domin jajanta wa jamaa bayan wasu yan bindiga sun kona wasu matafiya 23 kurmus wadanda suke kan hanyarsu ta yin kaura saboda yawaitar hare-hare a yankinsu na Sabon Birni.
Wani abu da ya tunzurra jamaa wajen sukar shugaban kasar shi ne yadda ya tafi birnin Lagos domin kaddamar da littafin wani dan siyasa yayin da jamaar Sokoto suke ci gaba da alhinin mutuwar mutanen.
Daga bisani Shugaba Buhari ya aika da sakon taaziyya a kan kisan mutanen sannan ya tura da tawaga mai karfi domin yin jaje a madadinsa.
Sai dai Dingyadi ya ce: “Wadannan abubuwa [hare-hare] kullum suna faruwa, kuma bai yiwuwa a ce shi Shugaban kasa ya iya zuwa duk wuraren da abubuwan suka faru…ai idan ka tura wakili kamar kai ne ka je.”
Read Also:
Bugu da kari Alhaji Maigari Dingyadi ya ce jami`an tsaro na tsara dabarun daƙile hare-haren, kuma ba da daɗewa ba za a samu sauƙin hare-haren da `yan fashin daji ke kai wa al`ummomi a daukacin Arewa maso Yammacin ƙasar.
Sai dai a martanin da suka mayar, masu ruwa da tsaki a Sabon Birnin jihar Sokoton sun ce ba zuwa jaje ne a gabansu ba, burinsu shi ne a kawo karshen kashe-kashen da ake kai musu ba ji ba gani.
A cewar Honourable Aminu Boza ɗan majalisar dokoki mai wakiltar Sabon Birni a majalisar jihar Sokoto,” ba shakka babban ayarin Shugaba Buhari ya zo ya gana da mu, sai dai ba wannan ne muradinmu ba.”
” Mu abin da muke so a daukar mana mataki… a karamar hukumata an kashe daruruwan mutane gwamnatin tarayya ba ta dauki kowane irin mataki ba, amma an kashe mace daya mai tallar ruwa a Legas gwamnatin tarayya ta dauki mataki har Shugaban kasa ya fito ya ce ya bai wa jami’an tsaro dama su nemo wadanda suka kashe wannan mata,” a cewar Honourable Aminu Boza.
Wani kisan wulaƙanci da `yan bindiga suka yi wa wasu matafiya a jihar Sokoto makon da ya wuce ta hanyar kona su ya sosa ran `yan kasar da dama, wanda ya janyo suka ga gwamnatin Shugaba Buhari.
Abin da ya kara fusata ‘yan kasar shi ne Shugaban ya tafi jihar Legas a daidai wannan lokaci don kaddamar da littafin tarihin rayuwar Bisi Akande, wanda sananne ne a kasar.