Biyan Bashi: ‘Yan Fansho Sun Bayyana Shugaba Buhari a Matsayin Jajirtaccen Shugaba Dake Sauraron Matsalolin Al’ummarsa
Yan fansho sun nuna matukar jin daɗinsu ga shugaba Buhari a wata wasika da suka rubuta masa.
Yan fanshon ƙarkashin kungiyarsu ta kasa sun rubuta wasikar godiya da jinjina ga shugaban.
Wannan dai ya biyo bayan umarnin da Buhari ya bayar na biyan yan fansho bashin da suke bi na shekara biyu.
Abuja:- Ƙungiyar yan fansho ta ƙasa ta rubutawa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari wasika ta musamman domin jinjina masa, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.
Wasikar yan fanshon dai godiya ce da fatan alkairi biyo bayan biyansu wasu kuɗaɗe da suke bin gwamnatin tarayya bashi da shugaban yayi.
Takardar wasikar wacce take ɗauke da sanya hannun shugaban yan fansho na kasa, Elder Actor Zal, da kuma sakatarensa, sun jinjina wa shugaba Buhari bisa wanna namijin kokari.
Read Also:
Yan fanshon sun bayyana Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba dake sauraron matsalolin al’umarsa kuma wannan matakin yasa yan fansho cikin annashuwa.
Me wasikar yan fansho ta kunsa?
A cikin takardar da kungiyar yan fanshon ta rubuta zuwa ga shugaba Buhari, sun ce:
“A madadin shugabannin wannan kungiya da mabobinta baki daya muna mika sakon godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari, kan ba da umarnin biyanmu hakkokin mu na shekaru biyu.”
“Duk da halin matsin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, an ba da umarnin biyanmu na watanni 12, sai kuma wasu watanni 6 a watan Yuni, da kuma karin wasu watanni 6 da muke sa ran karba a kowanne lokaci.”
Shin gwamnati ta gama biyansu kenan?
Yan fanshon sun kara da cewa muna fatan nan gaba kaɗan mu samu ragowar hakkokinmu na tsawon watanni shida da ya rage.
Daga karshe yan fanshon sun kara jinjina ga shugaba Buhari, inda suka ce: “Bamu da kalmar da zamu gode maka da ita.”