Sabuwar Shekara: Shugaba Buhari Zai yi Jawabi Gobe da Misalin Karfe 7 Na Safe

Kamar yadda ya saba, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabin sabon shekara ga yan Najeriya gobe Juma’a, 1 ga watan Junairu, 2021 misalin karfe 7 na safe.

Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Alhamis a shafinsa na Tuwita.

Garba Shehu ya yi kira da gidajen talabijin, rediyo da jaridun yanar gizo su garzaya tashar NTA da FRCN domin haska jawabin.

“Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabin sabon shekara ga kasa ranar Juma’a. 1 ga Junairu, 2021 misalin karfe 7,” Garba Shehu ya bayyana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here