Shugaba Buhari ya Sanar da Karin Albashin Malamai

A kwanakin baya ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da yi wa malaman makaranta karin albashi na musamman.

Sai dai, gwamnatocin jihohi sun yi watsi da batun tare da sanar da cewa ba zasu iya kaddamar da tsarin ba.

Yanzu haka gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kafa kwamitin da zai bullo da hanyar tabbatar da sabon tsarin.

Gwamnatin tarayya, a ranar Alhamis, ta ƙaddamar da kwamiti don ƙirƙiro hanyoyin da za’a bi don cimma gyarawa malamai masu koyarwa a makarantun sakandire albashinsu.

Wannan cigaban ya zo ne bayan alwashi da romon baka da Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yiwa malamai lokacin bikin murnar Ranar Malamai ta duniya a birnin tarayya Abuja.

Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, da yake magana akan taron da aka gudanar a ofishinsa, ya ce; “kwamitin aiwatarwa na ƙasa me bibiya da gyara akan harkar koyarwa a Najeriya an kafa shine don inganta koyo da koyarwa a faɗin ƙasar nan.”

Kwamitin wadda babban sakataren ma’aikatar ilimi, Arc. Sonny Echono, ke shugabanta, ya rabu zuwa ƙananan kwamitoci 12 don mayar da hankali akan muhimman ɓangarori na musamman da suke buƙatar sa hannu da tallafawa.

Kwamitin da aka ƙaddamar ya fara bin hanyoyin aiwatar da sabbin tsare tsare wanda shugaban ƙasa ya furtasu kwana kwanan nan, wanda suke da nufin jawo masu ƙoƙari da ƙwaƙwalwa zuwa cikin harkar koyarwa.

A cewar FG, hakan zai bawa malamai ƙarfin guiwa wajen gudanar da ayyukansu da kuma fitar da gogaggun ɗalibai masu hazaƙa don bunƙasa cigaban ƙasa.

Wasu daga cikin tsare-tsaren sun haɗar da; Albashi na musamman ga malamai masu koyar da masu buƙata ta musamman.

Ƙara wa’adin barin aiki da shekarun koyarwa, Fansho na musamman ga malamai masu koyar da masu buƙata ta musamman, ƙarawa aikin koyarwa matsayi da cancanta ga malaman gwamnati da kuma bada alawus na musamman ga malamai.

Da yake ƙaddamar da kwamitin, Ministam Ilmi, Mallam Adamu Adamu, ya bada tabbacin bada dukkan wata gudunmawa da ake buƙata ɗon aiwatar da tsare-tsaren cikin tsanaki da nutsuwa.

A maganganun da yayi ya ce; “Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya yarda cewa harkar koyarwa ita ce babbar hanyar da zata habbaƙa ta kuma bunƙasa cigaba a ƙasa.

“Saboda haka, ilmi, sadaukarwa, da kuma iyawa sune nagarta da za’a ke dubawa kafin ɗaukar yayayyun ɗalibai daga manyan makarantunmu zuwa ajuzuwa, sai kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban ƙasa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here