Shugaba Buhari ya Kunyata Miliyoyin ‘Yan Najeriya Har da ‘Yan a Mutun APC – Dr. Hakeem Baba Ahmed

 

Shugaba Buhari ya kunyata miliyoyin yan Najeriya har da yan a mutun APC, Baba Ahmed.

Kakakin Dattawan Arewa yace sun yi nadamar kawar da Jonathan a 2015.

Ya yi kira ga jama’a su san irin wanda zasu zaba a 2023.

Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa ta yi nadamar yaki da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, don ganin cewa Shugaba Buhari ya ci zabe a shekarar 2015.

Kungiyar ta yi Alla-wadai da yadda Buhari ya kunyata miliyoyin yan Najeriya har da ‘yayan jam’iyyarsa ta All Progressives Congress da suka yi aiki tukuru don ganin ya ci zabe.

Saboda haka, kungiyar dattawan Arewan ta ce Shugaban kasan da za’a yi nan gaba ya kasance mutum wanda zai bi tafarki irin na Buhari ba.

Kakakin kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, yayi wannan jawabi a hirarsa da yan jarida a shirin ‘The Morning Show’ na tashar Arise TV ranar Talata.

A cewarsa:

“Shin akwai wani dan Najeriyan da Shugaba Buhari bai ba kunya ba yanzu, har da yan a mutun APC? Shin akwai wanda zai ce Buhari bai gaza ba?”

“Mun yi masa kyakkyawan zato, mun fadawa mutane, ‘Kuyi watsi da Jonathan, ku zabi Buhari, zai yi yaki da rashawa, zai magance matsalar tsaro, zai gyara tattalin arziki’ amma kalli inda muke yanzu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here