Shugaba Buhari ya Kafa Kwamitin Mika Mulkin Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin mika mulki ga duk wanda ya ci zaben 2023 na shugabancin kasa.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan tare da mambobin kwamitin a takardar da ya fitar.
Mustapha yace da kanshi zai kaddamar da kwamitin a ranar 14 ga watan Fabrairun 2023 da karfe 12 a dakin taronsa na Abuja.
Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa Kwamitin Fadar Shugaban kasa na mika mulki domin lura da tabbatar da mika mulki daga gwamnatinsa.
Sakataren Gwamnan Tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto
Read Also:
Kamar yadda yace, kwamitin ya hada da sakataren gwamnatin tarayya matsayin shugaba, yayin da sauran mambobin suka hada da shugaban ma’aikatan gwamnati na tarayya da babban sakataren ma’aikatar shari’a ta tarayya.
A ciki akwai sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, ofishin sakataren gwamnatin tarayya, babban mai bada shawara kan tsaron kasa, shugaban ma’aikatan tsaro, darakta janar na hukumar tsaron farin kaya, babban magatakardan kotun koli da kuma wakilain biyu da zababben shugaban kasan zai zaba.
“Sakataren gwamnatin tarayya ne zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata, 14 ga Fabrairun 2023 da karfe 12 na rana a dakin taron SGF.
“Dukkan mambobin da aka lissafo zasu halarci taron da kansu.”
– Mustapha ya sanar da hakan a takardar da daraktan yada labarai, Willie Bassey, ya saka hannu a madadinsa.
Karin bayani na nan tafe…