Najeriya: Shugaban Kasar ya yi wa Matasan da ke Bautar Kasa Goma ta Arziki
Shugaban hukumar NYSC, Janar Shuaibu Ibrahim, ya sanar da wani gata da shugaban kasa, Buhari, ya yiwa matasan da ke butar kasa.
A cewar Janar Ibrahim, shugaba Buhari ya bayar da umarnin a saka matasan da ke butar kasa a cikin tsarin inshorar lafiya ta kasa.
Kazalik, ya ce hukumar NYSC ta sake karfafa hadin gwuiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro ga matasa ‘yn bautar kasa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) a kan ta tabbatar da shigar da matasan da ke hidimatawa kasa cikin tsarin cin moriyar inshorar lafiya.
Babban darektan hukumar kula da shirin bautar kasa (NYSC), Janar Shuaibu Ibrahim, ya sanar da hakan ranar Litinin.
Read Also:
Janar Ibrahim ya bayyana cewa NYSC ta kara karfafa alakarta da hukumomin tsaro domin tabbtar da tsaron lafiyar matasan da ke shirin NYSC a duk inda aka turasu.
Shugaban na NYSC ya bayyana hakan ne yayin wani taro manema labarai da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja.
A cewarsa, hukumar NYSC ta na yaye matasa fiye da 300,000 a kowanne rukuni, wanda hakan ”ko shakka ya saka NYSC wani babban shiri na horon matasan Najerriya domin samun hadin kai da cigaba.”
“Ina son yin amfani da wannan damar domin sake mika godiyarmu ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bamu.
“Bayan haka, NYSC ta kammala shiri da hukumar NHIS domin shigar da matasan da ke hidimar kasa cikin tsarin cin moriyar inshorr lafiya kamar yadda shugban kasa ya bayar da umarni,” a cewar Janar Ibrahim.