Shugaba Buhari Bai yi Wani Alkawarin Mika Mulki ga Bola Tinubu ba – Osita Okechukwu
Osita Okechukwu, jigo a jam’iyyar APC ya ce babu wata yarjejeniya cewa Buhari zai mika wa Tinubu mulki a 2023.
Okechukwu, shugaban VON, ya bayyana hakan ne yayin martani kan ikirarin da Rufai Hanga ya yi na cewa akwai wannan yarjejeniyar.
Okechukwu ya kara da cewa Buhari ba mutum bane mai son yin yarjejeniya da mutane sai dai yana saka kyauta da tukwici.
Jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma shugaban muryar Nigeria, VON, Osita Okechukwu ya ce.
Shugaba Muhammadu Buhari bai yi wani alkawarin mika mulki ga jagoran jam’iyyar Ahmed Bola Tinubu ba, Daily Trust ta ruwaito.
Wanda ya kafa tsohuwar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC), kuma shugabanta, Senator Rufai Hanga, a baya bayan nan ya ce ‘akwai yarjejeniyar’ da ke nuni da cewa Buhai zai mika mulki ga Tinubu a 2023.
Read Also:
Hanga, wanda ya shugabanci daya daga cikin jam’iyyun da suka hadu suka kafa APC a 2014, ya ce wannan yarjejeniyar ce ta sa Tinubu ya cigaba da zama a APC bayan wa’adin Buhari na farko.
Amma, Daily Trust ta ruwaito cewa Okechukwu ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa babu wannan yarjejeniyar, ya kara da cewa Buhari bai cika yin yarjejeniya da mutane ba. Okechukwu ya ce:
“A matsayina na mamban tsohuwar jam’iyyar CPC, ban taba jin wannan yarjejeniyar ba, Shugaban kasa zai so ko bai cika yin yarjejeniya a hukumance ko akasin haka da kowa ba. Amma yana yaba kyauta da tukwici.
“Abin da na sani kawai shine ba domin wani matsala ta doka ba da Asiwaju ne zai zama mataimakin shugaban kasa.
“Domin shugabanin jam’iyyar mu suna gargadi kan tikitin Musulmi da Musulmi.
“Shugabannin jam’iyyar mu sun ce tikitin musulmi da musulmi irin ta Abiola da Kingibe a 1993 ba za ta yi aiki ba a yanzu domin abubuwa sun sauya a 2015.
Idan Buhari da Tinubu suka yi takara, abin zai canja. Haka ne yasa aka zaci Farfesa Yemi Osinbajo a madadinsa.”