Buhari Mutumin Kirki ne, Amma dai ba Shugaba ne Nagari ba Idan Aka Duba Yadda Yake Mulki – Kukah

Faston nan da ya yi kaurin suna wajen caccakar Buhari ya sake yin jawabi, ya ce ko Aisha Buhari ba ta goyon bayan Buhari.

Ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci ga fadar shugaban kasa kan martanin da ta yi na jawabansa na baya.

A bayan ya caccaki shugaba Buhari, inda yace mulkin Buhari ya raba kan ‘yan Najeriya da dama a shekarun nan.

Babban limamin cocin nan da ke tasa Buhari a gaba, Matthew Kukah, ya ce Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ita ma ta amince da abin da ya fada game da mijinta.

Kukah ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a safiyar ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

Bishop din yayin da yake karin haske ya bayyana cewa babu wani abu tsakaninsa da Shugaban kasa Buhari illa dai kawai manufofinsa da ko da kuwa matarsa Aisha ma ta ki aminta da su.

Kukah ya ce:

“Duk masu cewa na soki shugaban kasa, ban taba sukar halinsa ba. Duk abin da na yi magana a kai shi ne rashin iya tafiyar da al’amuransa daban-daban yadda ya kamata kuma daidai. Na karanci bambance-bambance a matsayin darasi don haka na san abin da nake magana akai.”

Ya bayyana cewa, ya yi imani da cewa Buhari mutumin kirki ne, amma dai ba shugaba ne nagari ba idan aka duba yadda yake mulki.

A cewarsa, yana matukar mutunta shugaban kasa da kuma halayensa da ya ce Buhari Buhari mutumin kirki ne amma idan ya kalle shi a matsayin shugaban kasa, to gaskiya ya gaza wajen gudanar da aikinsa.

Kukah wanda ya tabbatar da cewa yana magana kai tsaye da shugaban kasar ya ce sukar da yake yiwa gwamnati ba wani abu bane na kashin kai illa kishin ganin al’amura sun daidaita a kasar.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here