Shugaba Buhari ya Nada salisu Garba a Madadin Ishaq Bello a Matsayin Babban Alkalin Kotun Abuja

A ranar Laraba, 06 ga watan Janairu, ne mai shari’a Ishaq Bello, babban alkalin kotun Abuja, ya yi murabus.

Sakamakon ritayarsa ne shugaba Buhari ya amince da nadin Salisu Garba a matsayin madadinsa.

Sakamakon ritayar babban jojin ƙasar nan, mai Shari’a Ishaq Bello, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya baiwa Salisu Garba, muƙamin riƙon babban joji a babbar kotun kasa da ke Abuja, kamar yadda TheCable ta rawaito.

A wata takarda wacce daraktan sadarwa a ma’aikatar Shari’a na ƙasa ya fitar, ya ce alkalin alkalai na kasa (CJN), Mai Shari’a Ibrahim Muhammad, ne zai rantsar da Garba ranar Larabar nan.

“Sakamakon ritaya da mai girma Ishaq Bello ya yi a yau (Laraba), shugaba Muhammadu Buhari, GCFR, ya sahale da naɗin mai girma Salisu Garba a matsayin mai riƙo.”

“In Allah ya kai mu gobe ne (Laraba), mai girma mai Shari’a I.T Muhammad, CFR, zai rantsar da shi da misalin ƙarfe 2:00 na rana,” kamar yadda sanarwa ta bayyana.

Sabon alkalin da Buhari ya amince da nadinsa dan asalin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina ne.

Salisu Garba ya samu zama cikakken lauya a 1984 ya kuma kammala bautar ƙasa a shekarar 1985. A baiwa Garba muƙamin majistare a babbar kotu a 1989.

A 1997 ya sama babban rijistara a babbar kotun tarayya ya zama alkalin babbar kotun tarayya a 1998.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here