Shugaba Buhari ya Nada Sabon Shugaban NDE
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin Shugaban hukumar NDE.
Gwamnatin tarayya ce ta sallami Nasir Argungu, wanda ya kasance rike da mukamin daga kan kujerarsa.
Fikpo ya kasance darakta mafi girma a NDE bayan ficewar tsohon Darakta Janar na hukumar.
Gwamnatin tarayya ta nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar daukan ma’aikata, domin ya maye gurbin Dr Nasiru Argungu wanda aka dakatar daga matsayin a ranar 7 ga watan Disamba.
Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, ya tabbatar da nadin a wata wasika mai taken “nada ka a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar daukan ma’aikata.”
Read Also:
An kuma aika wasikar zuwa ga Fikpo a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba, a Abuja, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
“Biyo bayan umurni daga Shugaban kasa na saukewa Dr Nasiru Argungu nauyi a matsayin Darakta Janar na hukumar NDE, don haka ana umurtanka da ka ci gaba a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar har zuwa lokacin da Shugaban kasar zai tabbatar da nadin.
“Wannan ya kasance ne don tabbatar da ganin babu gibi a gudanarwar hukumar,” in ji ministan.
Mista Keyamo, wanda ya kuma kasance minista mai sanya ido a hukumar, ya ce umurnin ya fara aiki daga ranar 7 ga watan Disamba.
Ministan ya bukaci mukaddashin darakta janar din a kan ya tabbatar da gudanarwa yadda ya kamata a hukumar.
Sannan kuma ya umurce shi da ya tabbatar da Dr Nasiru Argungu ya mika masa dukkanin kayayyakin gwamnati da ke hannunsa yadda ya kamata.