Shugaba Buhari ya Amince da sababbin Naɗe-Naɗe a Ma’aikatar Ilimi

 

Shugaba Buhari ya amince da sake maida wasu shugabanni a wasu hukumomi dake ma’aikatar Ilimi.

Hakanan kuma Shugaban ya yi wasu sababbin naɗe-naɗe a wasu hukumomin ilimi masu muhimmaci na kasa.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar ilimi, Mr Bem Goong, ya fitar.

Abuja – Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin wasu sabbin shugabannin hukumomi dake karkashin ma’aikatar ilimi, kamar yadda Punch ta rawaito.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi ta ƙasa, Mr Bem Goong, shine ya sanar da sabbin naɗe-naɗen a wani jawabi da ya fitar.

Goong yace shugaban ƙasa Buhari ya amince da sake naɗa shugaban hukumar rijistar malamai (TRCN), Farfesa Josiah Ajiboye, karo na biyu kuma zango na ƙarshe da zai shafe shekara 5.

Hakanan Buhari ya amince da sake naɗa Farfesa Bashir Usman, a matsayin shugaban hukumar wayar da kan fulani ta ƙasa, a karo na biyu kuma zango na karshe da zai shafe shekara 5, kamar yadda this day ta rawaito.

Wane sabbin naɗe-naɗe Buhari ya yi?

Goong ya bayyana sabbin naɗe-naɗen da Buhari amince da su, waɗanda suka haɗa da shugaban hukumar bada ilimin matasa, Farfesa Akpama Ibar.

Sai kuma shugaban ɗakin bincike na ƙasa, Farfesa Chinwe Anunobi, da kuma shugaban manyan makarantun horar da malamai (NTI), Farfesa Musa Maitafsir.

A jawabinsa Boong yace: “Baki ɗaya sabbin naɗe-naɗen uku zasu fara aiki daga ranar 2 ga watan Satumba kuma kowannen su shine zangon farko da zasu shafe shekaru 5.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here