Shugaba Buhari ya Dawo Najeriya Bayan Gudanar da Umara a Saudiyya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma ƙasar bayan ziyarar kwanaki takwas a Saudiyya, inda ya gudanar da ibadar Umara.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ruwaito cewa a lokacin da shugaba Buhari zai bar Saudiyya ya samu rakiyar jami’an gwamnatin Saudiyya da sarakunan gargajiya da malaman addini na Najeriya zuwa filin jirgin saman birnin Jedda.
Read Also:
A cikin wata sanarwa da mai magana da shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban shafe kusan sa’o’i bakwai a jirgi daga Jedda zuwa Abuja sakamakon kauce wa bi ta sararin samaniyar Sudan saboda rikicin da ake yi a ƙasar.
Sanarwar ta ce shugaban ya biyo ta Eritrea, sannan ta Ethiopia, ta Kenya, ta Uganda, ta DR Kongo, ta Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sai kuma Kamaru, sannan ya ƙarasa Najeriya.
A ranar Alhamis da ta gabata ne shugaban ƙasar ya gudanar da ibadar Umara bayan da ya isa masallacin harami da ke birnin Makka, sannan ya ziyarci masallacin Annabi da ke Madina.
Haka kuma shugaban ƙasar ya kai ziyara wuraren tarihi a biranen Makka da Madina a ranakun Talata da Laraba.
A lokacin ziyarar tasa a ƙasa mai tsarkin shugaba Buhari ya yi taron shan ruwa da sarakunan gargajiya da malaman addini na Najeriya da suka je aikin umara