Sunayen Sababbin Kwamishinoni 3 da Shugaba Buhari ya Rantsar a Hukumar INEC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni uku a hukumar INEC makonni bayan majalisar dattawa ta tabbatar da su.
Sabbin kwamishinonin sun hada da Baba Bila daga arewa maso gabas, Sani Adam daga arewa maso tsakiya da Abdullahi Abdu daga arewa maso yamma.
Bayan rantsarwar, shugaban kasar ya kira taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na mako-mako a fadar gwamnati.
Aso-Rock, Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda uku na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).
Jaridar The Nation ta rawaito cewa an gudanar da bikin ne a takaice kafin fara babban taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na mako a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Read Also:
Legit.ng ta tattaro cewa wadanda aka rantsar sun hada da Dr Baba Bila mai wakiltar shiyyar arewa maso gabas, Farfesa Sani Adam, arewa maso tsakiya da Farfesa Abdullahi Abdu, mai wakiltar arewa maso yamma.
Rahoton ya ce a halin yanzu shugaban kasar yana jagorantar taron FEC na mako a dakin taro na ofishin Uwargidan Shugaban kasa a Fadar Shugaban Kasa.
Channels TV ta kuma rawaito cewa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo (SAN) da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, na cikin wadanda ke halartar taron a zahiri.
Akwai kuma ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed; babban lauya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami; da ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu.
Sauran sun hada da ministocin kudi, kasafin kudi da tsare -tsare na kasa, Zainab Ahmed; ayyuka da gidaje, Babtunde Fashola (SAN) da na harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbeshola.