‘Yan Bindiga Sun Sace Matan Aure  2 a Karamar Hukumar Kwali Dake Abuja

 

‘Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace matan aure biyu a kauyen Piri da ke karamar hukumar Kwali, Abuja.

Masu garkuwa da mutanen sun kai mamaya yankin ne da misalin karfe 11:22 na daren ranar Lahadi.

Zuwa yanzu dai basu tuntubi ‘yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su ba.

Birnin tarayya, Abuja – Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan aure biyu a kauyen Piri da ke karamar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin garin mai suna Emos Bako, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:22 na daren ranar Lahadi, lokacin da masu garkuwa da mutanen suka mamaye unguwar.

Ya ce sun shiga gidan da karfi suka sace wata mata kafin su ci gaba da sace wata mata a unguwar da ke makwabtaka, jaridar Daily Trust ta rawaito.

Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace, wanda ya so a sakaya sunansa, ya ce mijin daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su baya gida lokacin da lamarin ya faru, ya kara da cewa har yanzu ba a fara tattaunawa da masu garkuwa da mutanen ba.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya, ASP Daniel Y Ndiparya, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar za ta tabbatar da ganin cewa an ceto mutanen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here