Shugaba Buhari ne Ummul Aba’isin Duk Rikicin da Ake Samu na Rarrabuwar kawunan ‘Yan Najeriya – Ayo Adebanjo
Shugaban ƙungiyar yarbawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, ya ce shugaba Buhari ne babban wanda baison ganin cigaban Najeriya.
Adebanjo yace ba yadda za’a yi sojoji su ƙaƙabama yan Najeriya wannan kundin tsarin mulkin tun 1966 amma Buhari yaƙi yarda a canza shi kuma yace shi mai kishin ƙasa ne .
Yace shugaba Buhari da jam’iyyar sa ta APC sune ummul aba’isin duk rikicin da ake samu na rarrabuwar kawunan yan Najeriya.
Shugaban ƙungiyar yarbawa, Afenifere, Chief Ayo Adebanjo, yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shine babban maƙiyin haɗin kan Najeriya.
Adebanjo ya faɗi hakane a shirin safe na gidan talabashin ɗin Arise News mai suna ‘Morning show’.
Yace shugaban shine ya buɗe ƙofa ga duk wani rabe-rabe da ake samu a ƙasar nan saboda watsin da yayi da kiran da masu kaunar Najeriya ke masa na yin sabon kundin tsarin mulki.
Ya kuma kara da cewa sojoji ne suka ƙaƙaba wa yan Najeriya kundin tsarin mulki 1999 (wanda aka gyara), kuma ya zama wajibi a canza shi.
Kuma Ya zargi kundin tsarin mulkin da yin rashin adalci ga wasu yankunan ƙasar nan.
Read Also:
Ya ce sabon kundin ne kaɗai zai iya rufe bakin masu tsegumi irin su Nnamdi Kanu da Sunday Igboho kafin zuwan zaɓen 2023 kamar yadda PM News ta ruwaito.
Adebanjo yace:
“Tun da shugaba Buhari yaki sauraran masu kira da a canza kundin tsarin mulki, hakan ya jawo masu tsegumi suka cigaba da aikinsu daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Kuma hakan ne ya ƙara kawo rarrabuwar kai tsakanin yan Najeriya.”
“Wannan ya nuna ƙarara cewa Buhari shine babban makiyin haɗin kan Najeriya tunda yaki amincewa da buƙatar al’ummar da yake mulka.” Adebanjo ya zargi Buhari da boyayyar manufa saboda ƙin amincewarsa wajen sake fasalta Najeriya.
Yace matasan yanzun basu da hakuri kuma bazasu iya ɗaukar wannan wahalhalun ba waɗanda wannan kundin tsarin mulkin na yanzun yake jawo musu.
Yace:
“An ƙaƙaba ma yan Najeriya wannan kundin tsarin mulkinne a shekarar 1966, Kuma shine babban dalilin rikicin dake faruwa yanzun.”
“Dole mu canza fasalin ƙasar nan, mu maidata asalin tsarin mulkin jamhuriya kamar yadda iyayen mu suka yi kokarin gina ta.”
Daga ƙarshe yace ƙin amincewar shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC wajen sake sabon kundin tsarin mulki, ya bayyana cewa dashi da jam’iyyar sa sune manyan maƙiyan haɗin kan ƙasar nan.