Buhari ya Saka Sabon Shugaban INEC

Bayan ganin wa’adin mulkin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na neman karewa, Buhari ya sabunta nadinsa.

Kwatsam sai ga sanarwar sabunta nadin Farfesa Mahmood Yakubu a karo na biyu, inda zai kara yin wasu shekaru 5 a kan kujerar.

Duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ba-zata, hakan bai hana kowa tofa albarkacin bakinsa ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, don sake yin shekaru 5 a kan kujerar.

Bayan wa’adin mulkinsa na haramar karewa, shugaban kasar ya sake nada shi. Wasu suna kawo sunayen mutane da dama da suke tunanin shugaban kasa zai nada, ashe ba ta nan gizo ke saka ba. Idan ba’a manta ba, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya hau kujerar bayan saukar Farfesa Attahiru Jega.

Farfesa Mahmood, kamar yadda aka ga ya tafiyar da zabukan 2017, ya tafiyar da mulkinsa cikin adalci da natsuwa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shayar da kowa mamaki bayan kara nada shi a wannan kujera,matsayin, duk da kowa yasan kujera ce mai hatsari da kuma bukatar nutsuwa kwarai. Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here