Shugaba Buhari ya Baiwa Sabbin Sakatarorin Dindindin 3 da ya Naɗa Rantsuwar Fara Aiki
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya baiwa Sabbin sakatarorin dindindin uku da ya naɗa rantsuwar fara aiki a Abuja.
Buhari ya rantsar da sabbin Sakatarorin ne gabanin fara taron mako-mako na majalisar zartarwa FEC yau Laraba.
Ministocin gwamnatin Buhari da sauran mambobin FEC sun halarci taron, wasu kuma sun shiga ne ta fasahar zamani.
Abuja – Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci bai wa sabbin Sakatarorin dindindin uku da ya naɗa rantsuwar kama da aiki da shiga Ofis a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban ƙasan ya yi haka ne a ɗakin taron da ke fadar shugaban ƙasa gabanin fara taron majalisar zartarwa FEC na mako-mako yau Laraba.
Mai taimaka wa shugaban ta fannin kafafen sada zumunta, Buhari Sallau, ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
Read Also:
Sabbin Sakatarorin Dindindin ɗin sune, Lydia Shehu Jafiya daga jahar Adamawa, Udom Okokon Ekenam, daga jahar Akwa Ibom da kuma Farouk Yusuf Yabo, daga jahar Sakkwato.
Bayan kammala rantsar da mutanen, shugaban ƙasa Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa na wannan makon.
Ƙusoshin Gwamnati da suka halarci taron
Taron wanda ke gudana yanzu haka da muke kawo muku rahoto ya samu halartan Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikata, Folasade Yemi-Esan, da mai ba da shawara kan tsaro, Babagana Monguno.
Ministocin da suka hallara sun haɗa da na ma’aikatar kuɗi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Yaɗa labarai da al’adu, Lai Muhammed, da Ministan Abuja, Muhammed Bello.
Sauran sune: Ministocin ma’aikatun kasuwanci da zuba hannun jari, Otunba Niyi Adebayo, saadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Sheikh Isa Pantami, wutar lantarki, Abubakar Aliyu, Kwadugo da ayyukan yi, Chris Ngige, da kuma ma’aikatar jin kai, Sadiya Farouq.
Baki ɗaya sauran mambobin majalisar da basu samu halarta da kansu ba sun shiga taron ta hanyar amfani da fasahar zamani watau Virtually.