Gwamna Godwin Obaseki ya Bukaci Shugaba Buhari da ya Sallami Ministar Kudi da Tattalin Arziki, Zainab Ahmed

 

PDP ta na so Shugaban kasa ya sallami Ministar kudi da tattalin arziki.

Jam’iyyar adawar ta zargi Zainab Ahmed da karya kan batun buga kudi.

Daga baya CBN ta fito ta gaskata kalaman da Gwamnan jahar Edo ya yi Babbar jam’iyyar hamayyar Najeriya, PDP, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Ahmed.

Jaridar Punch ta ce jam’iyyar adawar ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ta hannun sakataren ta na yada labarai na kasa, Kola Ologbondiyan. Kola Ologbondiyan ya soki matakin da gwamnatin tarayya na karyata rahoton buga Naira biliyan 60 da babban bankin kasa na CBN ya yi domin a toshe gibi.

Jam’iyyar PDP ta yi tir da rawar da Ministar tattalin arzikin Najeriya, Zainab Ahmed, ta ke taka wa, ta zarge ta da kokarin yin rufa-rufa da yi wa jama’a karya.

Mai girma gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki, ya fara wannan bayani inda ya ce sai da gwamnatin tarayya ta sake buga Naira biliyan 60 a watan jiya.

Bayan gwamnan ya yi wannan magana, Ministar kudi ta fito ta karyata shi, ta ce sam gwamnatin tarayya ba ta buga karin kudi domin a kara wa jahohin kasar ba.

Daga baya gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya raba gardama, ya ce babban bankin kasar ya buga karin kudi domin a tallafa wa tattalin arzikin Najeriya.

A dalilin haka, PDP ta ce akwai bukatar a tsige Zainab Ahmed tun da gwamnan CBN ya fallasa yaudara, da boye-boye, da karyar gwamnatin nan ta APC mai-ci.

PDP ta ce tun da gwamnati za ta koma wa yawan cin bashi da buge-bugen kudi, ta tabbata cewa Muhammadu Buhari bai da dabarar da zai inganta tattalin arziki.

A cewar Ologbondiyan, maganar da gwamnan CBN ya yi, ta tabbatar da cewa gwamnatin APC ta rugurguza tattalin arziki, kamar yadda alkaluma su ke ta nuna wa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here