Shugaba Buhari ya Sauke Ministocinsa 2 Daga Mukamansu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba ya sauke ministoci biyu daga mukamansu.
Ministocin sune na ma’aikatar gona, Mohammed Sabo Nanono, da takwaransa na ma’aikatar wutar lantarki, Saleh Mamman.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin labarai, Femi Adesina, ne ya sanar da wannan.
Read Also:
Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a majalisar ministocinsa, inda ya sanar da sallamar wasu ministoci biyu, jaridar Daily Trust ta rawaito.
Ministocin da aka sauke sune na aikin gona, Mohammed Sabo Nanono da takwaransa na ma’aikatar wutar lantarki, Mamman Saleh.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kafofin watsa labarai, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, jaridar Tribune ta rawaito.
Ya ce an sauyawa karamin ministan muhalli, Mohammed Abubakar, waje zuwa ma’aikatar aikin gona yayin da karamin ministan ayyuka, Mista Abubakar Aliyu, zai zama ministan wutar lantarki.
Ya ce za a cike guraben da babu kowa kamar yadda tsarin mulki ya tanada.