Shugaba Muhammadu Buhari Zai Tafi Qatar

 

Shugaban Najeriya muhammadu Buhari zai tafi Qatar a yau Asabar, domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na biyar game da abin da ya shafi kasashe masu ƙarancin ci gaba wanda za a yi a Doha babban birnin Qatar.

Cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban na musamman kan harkokin yaɗa labarai Garba Shehu ya fitar, ya ce wannan ya biyo bayan saƙon gayyatar da Sarkin Qatar Sheik Tamim bin Hamad al Thani ya turo wa shugaban.

Taron wanda za a yi tsakanin 5 zuwa 9 gawatan nan an yi masa take ne da: “daga ƙasa mai yiwuwar ci gaba zuwa mai haɓɓaka” ana yi shi ne sau ɗaya cikin shekara 10.

Wata dama ce ga ƙasashe masu tasowa su samu taimako daga ƙasashen duniya domin samun cimma muraden ƙarni cikin gaggawa kuma su taimaka musu wajen samun ci gaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here