Shugaba Buhari ya Tattauna da Jonathan da Namadi
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo a fadarsa ta Aso Rock a ranar Talata 22 ga wata Disambar shekarar 2020.
Ya karbe su ne a lokaci dabandaban.
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ne ya sanar da ziyar Jonathan ta shafinsa na Twitter da misalin karfe 5.10 na yammacin Talata. A halin yanzu ba a bayyana dalilin ziyarar da tsohon shugaban kasar ya kai fadar gwamnatin ba.
Shugaba Buhari yayin ganawarsa da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a Aso Rock a ranar Talata yace ya ce Allah ne kadai zai iya saka idanu a kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kasar ya ce duk da hakan gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu tsaro da zaman lafiya a yankin na Sahel.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.
A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, “don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa’adinsa biyu.”
Adesina ya ce ya jiyo Buhari ya cewa, “Daga Daura na fito, kilomita kadan ke tsakanin mu da Jamhuriyar Nijar, don haka na dan san wani abu game da kasar. Shugaban kasarsu mai mutunci ne kuma mu kan tuntubi juna sosai. Ba zai wuce tsawon lokacin da kudin tsarin mulki ta diba wa shugabanni ba a kasarsa.
“Kazalika, muna da iyaka mai tsawon kilomita 1,400 wadda Allah ne kadai zai iya kiyaye ta yadda ya dace. Zan yi magana da shugaban kasar in bawa kasarsa gudunmawar mu. Ya zama dole muyi duk abinda zamu iya don kawo tsaro a yankin Sahel don duk zai amfane mu.”
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya taya Shugaba Buhari murnar ceto yaran makarantar Kankara da murnar cika shekaru 78 a duniya a makon da ta gabata.
Ya yi alkawarin ECOWAS zata tabbatar anyi zaben adalci cikin zaman lafiya a Jamhuriyar Nijar duk da matsalolin da ake fama da su a kasar, ya kara da cewa ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a harkar.