Buhari ya Tura Tawagarsa Zuwa Borno

Shugaban kasa Buhari ya aika wata tawaga zuwa Borno a kan kisan gillar da aka yi wa wasu manoma a jihar ta arewa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ne ya jagoranci tawagar wacce ta hada da kakakin Shugaban kasar, Garba Shehu da wasu ministoci.

Mayakan sun halaka akalla manoma 43 a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

Wata tawaga ta gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, sun isa garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Tawagar sun kai ziyarar jaje da ta’aziyya ne a kan kisan kiyashin da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a yankin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere ta jihar.

An tattaro cewa manyan jami’an gwamnatun sun isa garin Maiduguri a ranar yau Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

Labarin ziyarar nasu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin labaran Shugaban majalisar dattawan, Ola Awoniyi ya saki a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

A cewar sanarwar, mambobin tawagar sun hada da Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da ministan birnin tarayya, Mohammed Bello, da ministan sadarwa, Ali Pantami.

Sauran mambobin sun hada da mai ba kasa shawara a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno (mai ritaya), karamin ministan noma, Mustapha Baba Shehuri da kakakin Shugaban kasa, Mallam Garba Shehu.

Tawagar sun ziyarci Borno a madadin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin tarayya domin yin ta’aziyya ga iyalan mamatan, gwamnati da kuma mutanen Borno kan mummunan al’amarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here