Shugaba Buhari ya yi wa Dr Isa Pantami Ta’aziyya

 

Shugaban kasa ya jajantawa Sheikh Isa Ibrahim Pantami.

An yi jana’izar Aisha a ranar Talata a masallacin Annur da ke Wuse 2 a Abuja bayan sallar Zuhr.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’ziyyarsa ga Ministan sadarwa, Dr Isa Ibrahim Ali Pantami, bisa rashin diya da yayi ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2020.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa Buhari daga samun labarin mutuwar Aisha ya kira Dr Isa Pantami a waya yayi masa jaje.

Ya yi addu’a Allah jikanta kuma ya karawa iyalan Minista Pantami hakuri.

Yace: “Shugaba Buhari ya kira Ministan da yammacin Litinin, inda ya jajantawa dukkan iyalansa bisa wannan rashi.”

“Buhari ya yi addu’a Allah ya jikanta kuma ya azurta ta da Jannatul Firdausi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here