Sunday Igboho: Lauyan Igboho ya Bukaci Kotu  ta Bada Belin Shi Don ya Kula da Raunikan Jikinsa

 

Lauyan Igboho ya ce mutumin ya jigata sosai kuma yana bukatan ganin Likita

Ya mika bukata ga kotu a bashi beli don ya kula da kansa.

Igboho ya tsallake rijiya da baya yayinda DSS suka kai harin gidansa a farkon watan yuli.

Mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho, ya samu munanan raunuka lokacin da jami’an hukumar DSS suka kai masa hari gidansa dake Soka, Ibadan, jahar Oyo.

A ranar Alhamis, 1 ga Yuli, 2021, hukumar DSS ta kai samame gidan Igboho.

Lauyansa na kasar Benin, Ibrahim Salami, ya bayyana hakan a hirar da yayi ranar Talata, rahoton ThePunch.

Ya yi bayanin cewa har yanzu Igboho na jinyan raunuka.

A cewarsa, Sunday Igboho na bukatan a bashi beli saboda ya kula da kansa.

Salami yace, “Ina kira ga iyalansa da magoya bayansa suyi hakuri kuma su cika da addu’a.

Lokacin da suka kai hari gidansa a Najeriya, ya yi tsalle ne daga saman gini kuma kirjinsa ya samu rauni. Ya jigata sosai.”

“Kai ko tsayuwa ya gaza yi gaban Alkali. A zaune yayiwa Alkali magana. Yana bukatan a sakeshi saboda ya kula da kansa.”

Harin da DSS ta kai gidansa.

A harin da DSS ta kai, an damke abokansa 13 kuma an hallaka 2.

Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bayyana hakan a hirar da yayi da manema labarai cewa sun samu labarin Sunday Igboho na boye makamai a gidansa.

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here