Kungiyar Matasan Warri ta Yanke Hukuncin Bulala 40 ko Tarar N10,000 ga Mata Masu Shigar Banza

 

 

Matasan yankin karamar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta sun ɗauri damarar yaƙar shigar rashin ɗa’a da yan mata ke yi.

Ƙungiyar matasan ta yanke hukuncin Bulala 40 ko tarar N10,000 ga duk macen da aka kama ta yi shigar nuna tsiraici.

Sun ce ba zasu lamurci yanayin shigar da ‘yan matan ke yi da sunan wayewa ba, dole su koya nusu tarbiyya.

Delta State – Ƙungiyar matasa mai suna ‘Ubeji Youth and Employment Development’ da ke ƙaramar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta sun ɗauki matakin gyara tarbiyya a yankinsu.

Ƙungiyar ta cimma matsaya kuma ta amince da hukuncin bulala 40 ga kowace matashiyar budurwa da aka kama ta yi shigar rashin ɗa’a ta jan hankali a garinsu.

Jaridai Daily Trust ta ranar Asabar ta tattaro rahoton cewa ƙungiyar ta kuma bada zaɓin tarar N10,000 ga duk macen da aka kama da saɓa wa dokar shigar banza a yankin.

Sakataren ƙungiyar matasan, Mista Stanley Bomele, shi ne ya bayyana haka yayin da yake hira da manema labarai a jihar Delta.

Ya ƙara da cewa matasa sun yanke fara aiki mai taken, “Yaƙi da shigar banza,” a tsakanin matasan ‘yan mata a yankin, wanda ke neman zama ruwan dare.

Mista Bemele ya ce wannan matakin ya zama wajibi sakamakon yadda shigar mata ke ƙara lalacewa kullum, sun koma sanya kaya na rashin ɗa’a da rashin tarbiyya a yankin.

An haramta wa mata sa matsattsun kaya?

Bugu da ƙari, Sakataren ya sanar da cewa daga ranar, sun ta haramta wa mata sanya ƙananan Siket (Minisikets) da sauran matsattsun kaya da ke fito da surar jikinsu.

Ya yi gargaɗin cewa ba zasu lamurci ganin ‘yan mata na sanya irin waɗan nan kayan ba saboda su ne babbar ƙofar da ke haddasa yawaitar lalata da cin zarafin mata.

Ya ce yanzun da yawan matan yankin sun lalace wajen sanya kaya da sunan wayewa, da yawansu suna fitowa tamkar tsirara, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ce wannan aikin na hukunta duk wacce ta yi shigar banza zai ci gaba daga nan har zuwa lokacin da matan yankin zasu shiga taitayinsu, su riƙa shiga ta kamala.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here