Bulama ya Gargaɗi Masu Amfani da Tutar Rasha a Wajen Zanga-Zanga 

 

 

Daruruwan masu zanga-zanga sun bi titunan yawancin jihohin arewacin Najeriya da kuma Legas, a yayin da aka shiga rana ta biyar da fara zanga-zangar kuncin rayuwa a kasar.

An ga wasu masu zanga-zangar sun sake haduwa a wasu bangarori na Abuja da kuma Fatakwal da ke kudancin Najeriya.

A wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriyar da suka hada da Zamfara da kuma Kaduna, an samu fitowar masu zanga-zangar da dama a yau Litinin inda har wasunsu ke daga tutar Rasha.

Akwai wasu faifayen bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda wasu masu zanga-zangar ke rike da tutar Rasha tare da nuna damuwa a kan karuwar matsalar tsaro a yankunansu.

Ba a san dalilin kawo Rasha cikin zanga-zangar ba, to amma ana fargabar za a iya bai wa lamarin wata fassara ta daban.

Wasu masu sharhi a Najeriya, kamar Bulama Bukarti, sun yi gargadin cewa yawaitar amfani da tutar Rasha a zanga-zangar akwai babbar matsala.

Cikin shafinsa na X , Bukarti ya ce, “Ina bukatar masu zanga-zangar da su yi taka tsan-tsan,sannan kuma kada su bari wasu masu mummunar manufa su yi amfani da su wajen cimma mummunar manufarsu.”

A ranar Lahadi ne shugaban Najeriyar Bola Tinubu, ya gabatar da jawabi ga ‘yan kasar inda ya yi kira ga masu zanga-zangar kuncin rayuwar da su dakatar, abin da wadanda suka shiryata suka ce shugaban kasar bai tabo batutuwan da suke bukata ba a yayin jawabin nasa abin da ya kara tunzurasu ke nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here