Gwamna Buni ya ɗage Haramcin Hawa Babura a Yankunan Jihar Yobe Bayan Shekara 11
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya sanar da ɗage haramcin amfani da babura a faɗin ƙananan hukumomi bakwai na jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin tsaro Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam ya fitar wadda kuma aka raba wa manema labarai a Damaturu a yau Litinin.
A cewarsa, baburan za su yi aiki daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a kowace rana. Ya ce baburan ba za su ɗauki mutum fiye da ɗaya ba ko yin achaba.
Read Also:
Ya kuma yi kira ga dukkan waɗanda ke da babura a ƙananan hukumomin da abin ya shafa, da su tabbatar da cewa sun yi musu rajista.
Gwamnatin jihar ta kuma bai wa masu baburan umarnin cewa su yi aiki a iya ƙananan hukumomi da suke ba tare da shiga wasu wurare ba, inda ta ce duk wanda aka samu da laifin take umarnin, zai fuskanci hukuncin da ya kamata.
A shekara ta 2012 ne dai lokacin gwamnatin Ibrahim Gaidam, aka sanya haramci kan amfani da babura a faɗin jihar ko achaba da nufin dakile yunkurin amfani da su wajen aikata muggan ayyuka, musamman lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a jihar.
Sai dai gwamna Mai Mala Buni ya ɗage haramcin a kan wasu ƙananan hukumomi 10 cikin 17 na jihar a watan Janairun 2022.