Tukur Buratai: Jawabin Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasar Najeriya, a Gurin Taron Bankwana da Aiki

 

Tsohon babban hafsan sojojin kasar Nigeria, Tukur Buratai, ya ce kaunar da mahaifinsa ke yi wa Buhari yasa Buhari ya nada shi mukaminsa.

Janar Tukur Buratai (mai murabus) ya yi wannan jawabin ne a wurin taron karramawa da aka shirya masa na bankwana da aiki.

Ya ce mahaifinsa wanda shima tsohon soja ne ya kasance mai kaunar Buhari don haka yana kallon nadin da aka masa a matsayin tukwici ga mahaifinsa.

Tsohon babban hafsan sojojin kasar Najeriya, Lt. Janar Tukur Buratai (mai murabus) ya danganta nadinsa a matsayin shugaban sojojin saboda kaunar da mahaifinsa ke yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewarsa, nadin da aka masa a watan Yulin shekarar 2015 sakayya ne ga mahaifinsa Yusuf Buratai da Buhari ya yi masa, The Punch ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa mahaifin Buratai shima jami’in soja ne a rundunar Royal West African Frontier Force kuma yana daga cikin sojojin da suka yi yakin duniya na II a Burma.

Tsohon shugaban sojojin ya mika godiya ga shugaban kasar bisa damar da ya bashi na yin aiki a matsayin shugaban sojoji, ya kara da cewa ya yi aikinsa iya kokarinsa.

Ya kuma kara da cewa duk da cewa rike mukamin shugaban sojoji abu ne mai tattare da kalubale, shugabanin sojojin sun yi nasara, ya kara da cewa, “na yi murabus amma ban gaji ba Insha Allah.”

Buratai ya ce, “Mahaifina masoyin shugaban kasa ne kuma nadin da aka min matsayin shugaban sojoji, tukwici ne na kaunar da mahaifina ke yi wa shugaban kasa.

“Kamar yadda aka sha fada maka (ni da shugaban kasa) mun hadu a N’djamena kuma ya ga cewa ni ne ya dace in zama shugaban sojojin kasa a wannan lokacin mai muhimmanci da tarihi a kasar mu.

“Kuma ina farin cikin cewa na yi iya kokari na kuma na yi aiki na bisa kwarewa da biyaya ga kasata kuma zan cigaba da yi masa da kasa na da al’umma na hidima.”

Buratai ya yi wannan jawabin ne wurin taron karramawa da aka shirya masa na bankwana da aiki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here