‘Yan Bindiga Sun Budewa Motar Gawa Wuta

 

‘Yan bindiga sun tare motar daukar gawa sun sace kanin marigayin da ake dauke da gawarsa.

Yan bindigan sun kuma kashe wani direban mota da ke biye da motar daukar gawar.

Masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan biyar Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a ranar Asabar 6 ga watan Fabrairu sun tare wata motar daukar gawa a babban titin Benin da ke jahar Edo sannan suka sace kanin da ke hanyarsa zuwa Enugu don yin jana’zar yayansa.

Duk da cewa ba su sace direban motar daukan gawar ba, harsashi ta kashe direban motar da ke bayan motar daukar gawar sakamakon bude wuta da yan bindigar suka yi.

Wani mazaunin garin Ahor a kan babban titin, mai suna Osamudiamen Odia ya shaidawa Premium Times cewa yana daya daga cikin wadanda suka ceto direban da ya fada cikin kwata bayan arangama da masu garkuwa.

Odia ya ce;

“Da ganin motar daukar gawar, yan bindigan sun bude wuta amma direban ya yi sa’a ya harsashin bai same shi ba.

Amma harsashin ya samu direban motar da ke bayansa inda matukin motar ya mutu nan take.

“Harbin bindigan ya tilastawa direban ya yi tsayawar gagagwa kuma ya fada cikin kwalbati.

Yan bindigan sun sace kanin mamacin da ke zaune a gaban mota sun shiga daji da shi.

“An dakatar da tafiyar saboda motar daukar gawar ta lalace. An kai gawar zuwa wani dakin ajiyar gawa a wata asibiti da ke Benin/Auchi a birnin Benin.”

Yayin da an gano cewar masu garkuwar sun nemi a biya su Naira miliyan 5 kudin fansa, mai magana da yawun yan sandan jahar, Chidi Nwabuzor ya ce an kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here