Burina na Siyasa ya fi Kasuwa a Arewacin Najeriya Fiye da Kowane Yankunan Kasar Nan – Rochas Okorocha
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Rochas Okorocha ya bayyana yankin da aka fi sonsa da kuma girmama shi a Najeriya.
Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce duk ‘yan takara ya yi fice saboda ana son sa a Arewa fiye da ko ina, hakan kuma na iya ba shi damar samun nasara a zaben 2023.
Okorocha ya lura cewa yana da karfin kayar da dan takarar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, har ma a jiharsa ta Adamawa a zabe mai zuwa.
Abuja – Tsohon gwamnan jihar Imo kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, ya ce burinsa na siyasa ya fi kasuwa a Arewacin Najeriya fiye da kowane yankunan kasar nan, inji rahoton Daily Trust.
Okorocha ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana kan batutuwan da suka shafi zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki.
Okorocha dai na fuskantar tuhume-tuhume 17 bisa zargin karkatar da kudade daga asusun hadin gwiwa na gidan gwamnatin Imo da na kananan hukumomi zuwa wasu kamfanoni masu zaman kansu tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016.
Bisa kamun da ya sha, kadan ya hana ya rasa damar tantancewar shugabannin APC na ‘yan takarar shugaban kasa da aka gudanar, rahoton Independent.
An tantance Okorocha ranar Talata
Read Also:
Bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Okorocha a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, ya nufi wurin da aka gudanar da aikin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na APC.
Game da cancantar sa na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Okorocha ya ce:
“Abin tambaya a yanzu shi ne: wane ne mutumin da zai iya lashe kuri’u kamar NA Buhari don ya kayar da wannan mutumin? Abin da ya kamata ya shagala a tunanin APC kenan.
“Kuma duk wani abu da ya tafi da wata fahimta, to, gazawa ce a wajenmu, kuma abin da ya kamata mu sani kenan, wane dan Najeriya ne zai iya samu kuri’u daga Arewa domin kawai abin da PDP ke alfahari da ita a yanzu shi ne su jawo kuri’un daga Arewa, gaskiya ne hakan.
“Kuma ba lallai Shugaba Buhari ya sake sake tsayawa zabe ba saboda yawancin mutanen da suka ci tikitin APC a Arewa sun samu ne saboda Shugaba Muhammadu Buhari.
“Kuma a matsayinsa na shugaban kasa da ya yi shekara takwas da kalubalen da ya fuskanta, watakila ba zai iya kawo wadannan kuri’u ba, kuma ba zai sake tsayawa zabe ba, don haka kuna da kalubale. Don haka sai a nemi wanene wancan mutumin da Arewa za ta iya duba ta ba shi kuri’a?
“Kuma ina ganin ni ne wannan domin na fi karbuwa a Arewa fiye da ko’ina. Ni masoyin Arewa ne.”
Okorocha, wanda shi ne Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, jami’an EFCC sun kama shi a gidansa da ke Abuja a ranar 25 ga watan Mayu.