Burodi Zai Shiga Jerin Abinci Masu Tsada – Shehu Sani

 

Dan fafutuka, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan tasirin da harajin da aka daura kan burodi zai yiwa al’ummar jihar Kogi.

Sani ya ce yanzu Burodi zai shiga jerin kayan abinci masu tsada sakamakon haka.

Har yanzu yan Najeriya na kuka kan hauhawar farashin shinkafa Har wa yau, sanya kudin haraji kan Burodi a jihar Kogi na cigaba da fuskantar suka daga wajen yan Najeriya.

Daya daga cikin wadanda sukayi tsokaci kan lamarin shine tsohon Sanata, Shehu Sani, wanda ya bayyana cewa wannan haraji zai sabbaba hauhawar farashin Burodi.

Shehu Sani ya ce Burodi zai shiga jerin abincin alfarma a jihar Kogi. Sanata Shehu a maganar da yayi ranar Juma’a 13 ga Nuwamba ta shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa Burodi zai fara tsada a jihar Kogi, kaman shinkafa da albasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here