‘Dan Najeriya da Bashi da Abinci ya Buga Caca da N50 Kacal ya Samu N4.8m
Da naira hamsin kacal, wani ‘dan Najeriya mai matukar sa’a ya zama miloniya a cacar da ya yi nasara kwatsam.
Mutumin, wanda bai da cin yau balle ba gobe ya samu nasara a caca, inda ya samu N4.8 miliyan take yanke.
‘Yan caca da dama sun taya shi murna yayin da suke ta wallafa takardar shaidar nasararsa a yanar gizo.
Wani mutumi ‘dan Najeriya ya yi nasarar samun makudan kudi N4.8 miliyan a cacar da ya saka N50.
Wani mai bada dabarbaru game da caca, @bossolamilekan1, ya wallafa takardar nasarar da mutumin ya yi a dandalin Twitter yayin da ya taya shi murna.
Haka zalika, mutumin ya wallafa hirarsa da mutumin, inda ya bayyana yadda bai da abun sanya wa a baka a daren da ya gabata.
Mutumin ya nuna jin dadi gami da godiyarsa ga bossolamilekan1, inda a cewarsa ya taimaka masa da salon dabarbarun caca.
Kamar yadda wallafar @bossolamilekan1 ta bayyana:
Read Also:
“Ba zan taba daina wallafa manyan nasarori ba. “Tabbas lokacin ka ne kayi nasara daga caca nan ba da jimawa ba, ka sake wallafa wa sannan kayi jinjina idan ka yarda da hakan.”
Martanin ‘yan soshiyal midiya
@AdesayoFasoro ya ce:
“Abun dariya. Wannan sa’a ne. Yin Arziki nan da nan ba abu bane mai sauki.”
@JanellEmerald ta ce:
“Na kasa magana…” Terencel8 ta ce: ”
@bossolamilekan1 ka ga abun da nake nema kai wannan mutumin ya fita daga kangin keburan baba taya ya iya cire duk wadannan abubuwan, @bossolamilekan1 duk lokacin da ya buga caca kawai ka wallafa mana.”
@__twenty23 ta ce:
“Nima wata rana zan yi babbar nasara daga cacarka, kuma in turo maka kudi kyauta.”
@Eshious ta ce:
“N50 ta koma 4m, wannan ya wuce abun mamaki 50,000. Kai..ina rokonka da ka wallafa hoton wannan, don mu ga wanda ya zaba ya yi nasara. Ina rokonka…”
@ALVIN904575201 ya ce:
“Ka gani ko, idan Ubangiji ya so canza labarin mutum irin haka, zai kawo wani abun mamaki ne. Mutumin da bai da kudin siyan abincin daren da ya gabata ya zama miloniya a daren yau da N50 kacal.”
@Gabby_real1:
“Wadannan mutanen su dinga aje mana dabarbarunsu don muma mu buga namu cacar.”