Mike Ozekhome ya Caccaki FBI Kan Umarnin Kama Abba Kyari
Wani babban lauya a Najeriya ya caccaki FBI kan umarnin kame jami’in dan sanda Abba Kyari.
Lauyan ya ce, FBI ba ta da ikon tasa keyar Abba Kyari zuwa Amurka ba tare da bin ka’ida ba.
Ya bayyana yadda ya kamata Amurka ta bi a hankali wajen gabatar da tuhuma yadda ya dace.
Babban Lauyan Najeriya, Mike Ozekhome (SAN), ya ce tilas Amurka ta gabatar da bukatar neman a mika mata mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari ta hanyar da ta dace.
Cibiyar Binciken Manyan Laifuka ta FBI ne ta zargi Kyari a wata tuhumar zamba da Ramon Abbas wanda kuma ake kira Hushpuppi ke fuskanta a Amurka.
Tuhumar Kyari ta biyo bayan umurnin kama shi daga wata kotun Amurka a gundumar tsakiyar California.
Read Also:
Da yake mayar da martani kan lamarin, Ozekhome ya ce hukumar FBI ba ta da ikon zuwa Najeriya haka kawai don kama Kyari ba tare da bin ka’ida ba.
Ya shaida wa Arise News a ranar Litinin, 2 ga Agusta cewa:
“Lokacin da Amurka ta nemi Abba Kyari, na ji mutane suna cewa FBI na da ikon kama Abba Kyari. A’a, ba zai yiwu a iya yin hakan ba. Najeriya kasa ce mai cin gashin kanta komai raunin da muka shiga.
“FBI ba ta da ikon zuwa nan haka kawai ta dauki Abba Kyari. Dole ne a bi tsarin fitar da mutane kamar yadda aka fada a cikin Dokar Kaddamar da Dokokin Tarayyar Najeriya ta 2004. Dole ne a duba Sashe na 2, 4, 5, 6, 7, 8, da 9 na dokar da aka yi.
Da yake karin haske, Ozekhome ya yi nuni da cewa wannan ba shine karon farko da Najeriya za ta fuskanci shari’ar tasa keyar wani dan ta ba.
Amma, ya koka da cewa batutuwan da suka shafi Kyari, dan awaren Yarabawa, Sunday Igboho, da jagoran haramtacciyar kungiyar aware ta IPOB, Nnamdi Kanu duk sun faru ne a lokaci guda.