Rikice ya Tsinke Tsakanin ‘Yan Kungiyar Shi’a da Jama’ar Yankin Dorayi Babba a Jahar Kano

A ranar Litinin, an ruwaito barkewar rikici tsakanin jama’an yankin Dorayi Babba a jahar Kano da mabiyar kungiyar IMN da aka fi sani da mabiyar akidar Shi’a.

Wannan rikici ya barke ne yayinda yan unguwar sukayi yunkurin hana yan Shi’an gudanar da taronsu ‘Ghadeer’ a unguwar.

Rahoton Premium Times ya bayyana cewa yan Shi’an sun shirya gudanar da taron ne a kan fili mallakin wani mutumi wanda shima dan Shi’a ne amma aka hanasu.

Majiyoyi a unguwar sun bayyana cewa dattawa a yankin sun bukaci mai filin ya sayar da filin saboda basu son yadda yan Shi’a ke taruwa a wajen.

Wani mazauni unguwar, Bilyaminu Abubakar, ya bayyanawa PT cewa: “Wasu dattawa sun bayyana cewa hankalinsu bai kwanta da yadda yan Shi’a ke taruwa a wajen ba.

Mai filin yace N50,000,000 zai sayar da filin amma sunce N12,000,000 zasu iya bashi.”

Yace lokacin da wasu daga cikin yan Shi’an suka isa wajen don taron ranar Litinin, wasu matasa suka kalubalancesu, kawai sai aka cakume da rikici.

Wani mai suna Aminu Miko yace: “Mutan unguwar sun kona wata mota mallakin Saleh Haruna kurmus.”

Ya kara da cewa mutane da dama sun jigata. Kakakin hukumar yan sandan jahar, Abdullahi Kiyawa, yace tuni an damke mutum hudu dake da hannu cikin rikicin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here