ALLAH ya yi wa Tsohon Ministan Noma, Malami Buwai Rasuwa

Gwamnatin jahar Zamfara ta tabbatar da mutuwar tsohon ministan noma, Malami Buwai.

Gwamna Bello Matawalle ya bayyana kaduwarsa kan rasuwar dattijon dan majalisar wanda ya rasu a babban birnin jahar Zamfara.

Ba a bayyana ciwon da ya yi sanadiyyar mutuwar Malami Buwai ba a lokacin kawo wannan rahoton Tsohon ministan noma, Malami Buwai, ya rasu bayan doguwar jinya.

TVC News ta rahoto cewa Buwai ya mutu a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, a Gusau, babbar birnin jahar Zamfara.

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana rasuwar tsohon ministan a matsayin babban rashi ba ga jahar Zamfara kadai ba har ma ga ƙasar baki ɗaya.

A cewarsa, Buwai ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban Zamfara musamman wajen taimakon marasa galihu.

Matawalle ya roki Allah da ya gafarta kurakuran marigayi ministan sannan ya baiwa iyalansa karfin gwiwa na jure rashin.

Gidan Rediyon Najeriya Kaduna ya ruwaito cewa an binne marigayin a makabartar Gusau bayan sallar jana’izar da babban limamin masarautar Gusau, Liman Dan-Alhaji Sambo ya jagoranta.

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, da manyan jami’an gwamnati sun halarci jana’izarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here