CACOVID ta Kashe Kimanin N25bn – Gwamnan Babban Bankin Najeriya

 

A shekarar 2020, bayan gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu sun bada gudunmuwar kudade na raba tallafi ga talakawa.

Kamfanonin sun radawa kansu suna gamayyar yaki da Korona wato CACOVID.

Gwamnan CBN ya bayyana cewa CACOVID ta kashe kimanin N25bn.

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa yunkurin da kamfanoni masu zaman kansu sukayi na raba kayan tallafin Koronan bilyan 25 ya taimakawa talakawa sosai.

Punch ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne a shirin kaddamar da wani Fim mai suna ‘Unmasked’ ranar Juma’a a jahar Legas.

Emefiele, wanda ya samu wakilcin mukaddashin diraktan sadarwa na CBN, Osita Nwamsobi, ya bayyana cewa wadannan kamfanoni masu zaman kansu sun hada cibiyoyin killace masu Korona 39 a fadin tarayya.

Yace, “Akan wannan mun bada bashin N83.9bn ga kamfanonin hada magani da Likitoci, kuma hakan na taimakawa wasu ayyukan bincike 26 da samar da magani 56 a fadin tarayya.”

“Hakazalika mun samu nasarar janyo hankalin masu ruwa da tsaki a Najeriya ta gamayyar CACOVID, wanda hakan ya taimaka wajen samar da kayan tallafin N25bn ga gidajen da annobar ta shafa da kuma kafa cibiyoyin killace masu cutar guda 39 a fadin tarayya.”

Wadannan kamfanoni da suka bada gudunmuwa sun hada da Dangote, BUA, bankin Access dss.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here