Rundunar Sojin Ƙasa ta Cafke Chiwetalu Agu Yayin Nuna Goyon Baya ga Ƙungiyar IPOB

 

Rundunar sojojin ƙasan Najeriya ta cafke sanannan ɗan wasan ƙwaikwayon Nolly Wood, wato Chiwetalu Agu a yayin da ya ke tunzura al’umma da kuma neman goyo baya ga haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB.

An kama shi ne sanƴe da suturar ƴan ƙungiyar a inda ya ke kira ga al’umma da su shigo a yi tafiya da su a haramtacciyar ƙungiyar.

Ko da yake ya nemi yin turjiya a yayin cafke shi, amma rundunar sojojin ba ta tilasta ko ta ci zarafin sa ba.

Ko da yake rundunar sojojin ƙasan ta na sane da ƴancin ƴan ƙasa na zirga zirga da furuci ba tare da tsangwama ba kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.

To bai kamata wani mutum ko ƙungiya ya saɓa wa dokar ƙasa ba, ta hanƴar tunzura jama’a domin take doka da oda.

Kamata ya yi a yi la’akari da muhimmancin zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Kamar yadda aka sani dai, ƙungiyar IPOB maramtacciya ce.

Saboda haka, duk wani mutum ko ƙungiya da ke ɗaukaka matsayin IPOB ya saɓa wa kundin tsarin ƙasa.

Musamman yadda yanayin tsaro yake a yankin kudu maso gabas, da kuma Atisayen GOLDEN DAWN da ke gudana, halin Chiwetalu Agu ya nuna amincewa da goyon baya ne ga haramtacciyar ƙungiyar.

Saboda haka ne aka cafke shi kuma a na yi masa tambayoyi. Yana kuma da fa’ida da mu bayyana zargin cewa an tozarta shi ƙariya ce maras tushe, wadda ya kamata ayi watsi da ita.

Rundunar sojojin ƙasan ba za ta sa ido haramtacciyar ƙungiyar IPOB da masu tallafa ma ta su raba kan ƙasa da gurɓata halin tsaro ba. Domin maslahar ƙasan ya fi muhimmanci akan fifita ƙabilanci da ɓangaranci.

Rundunar sojojin ƙasan na gargaɗin mutane da ƙungiyoyi da su guji dukkan wani ɗabi’a da zai haifar da tashin hankali a yankin.

Ana kira ga jama’a masu bin doka da oda a yankin da su ci gaba da gudanar da al’amuran su na yau da kullum, domin rundunar na shirye ta hukunta masu shirin tayar da hankalin al’umma.

Ana kuma ƙara kira ga jama’a da su baiwa hukumomin tsaro haɗin kai domin ci gaba da samar da zaman lafiya a yankin.

 

BIRGEDIYA JANAR ONYEMA NWACHUKWU
DARAKTAN HULƊA DA JAMA’A NA RUNDUNAR SOJOJIN ƘASAN NAJERIYA
7 OKTOBA 2021

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here