Kaddamar da Shettima: Kungiyar CAN ta Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Sojan Gona da Sunan ta

 

Kungiyar CAN, ta nuna takaicinta kan sojan gona da sunan ta da wasu mutane da ta ce jam’iyyar APC ta dako haya suka yi a yayin kaddamar da Shettima.

Barista Joseph Bade Daramola, sakataren kungiyar CAN din na kasa ne ya yi wannan gargadin a birnin tarayya Abuja.

Daramola ya ce abin takaici ne yadda jam’iyyar da ta nuna cewa Kiristoci ba su da muhimmanci amma kuma ta dauki hayar wasu fastoci da ba a sani ba don yin sojan gona da sunan CAN.

Kungiyar Kiristoci Najeriya, CAN, ta nesanta kanta daga kaddamar da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, tana cewa wadanda aka gabatar a wurin a matsayin shugabanin coci ‘ba su san su ba’.

Sakataren CAN na kasa, Barista Joseph Bade Daramola, ya bada wannan gargadin a ranar Alhamis a birnin tarayya, Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana rashin jin dadinsu kan tabargazar da wasu yan siyasa ‘wadanda suka yi ikirarin cewa kiristoci ba su da muhimmanci a gwamnati da siyasa suka tafi suka dako hayan bishop, fastoci don yi wa shugabannin CAN sojar gona a taron siyasan.

“Ba za mu amince da hakan ba, abin ki ne kuma sabo ga Allah. Idan suna cewa Kiristoci ba su da muhimmanci wurin zabe don mene suke musu sojan gona a wurin taron su?”

“Za mu bar su da al’umma su musu shari’a. Abin da suka aikata ya nuna wa mutane ko su wanene da abin da za su iya mana baki daya.

“Muna bukatar jam’iyyun siyasa kada su yi watsi da batun addini, musamman a Najeriya ta yau a lokacin da ake watsi da kirista.

Aikin da muke nema hakki ne da ke cikin kundin tsarin mulki kuma watsi da shi taka kundin tsarin mulki ne musamman ‘Federal Character Act,” in ji Daramola.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here