ka Cancanci Yabo – Dattawan Arewa ga Sarkin Musulmai
Sarkin Musulmi ya bayyana cewa Arewacin Najeriya ne wuri mafi hadarin zama yanzu.
Wasu dattawan Arewan sun ce lallai gaskiya mai alfarma a fadi.
Sun yi kira ga sauran shugabannin Arewa su bude mukulle bakinsu su tofa nasu albarkacin.
Dattawan Arewa sun jinjinawa mai alfarma sarkin Musulumi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, kan abind asuka siffanta matsayin fadin gaskiya kan lamarin tsaro ya tabarbare a yankin.
A cewar dattawan, matsayar Sarkin Musulmi ne gaskiyar magana kan rashin tsaro a Arewa, kuma shine musababbin matsalar tsadar abinci da ake fama da shi a kasar gaba daya.
Read Also:
Dattawan karkashin gamayyar dattawan Arewa wajen neman zaben lafiya da cigaba, a jawabin da suka saki ranar Asabar, sun ce Sarkin Musulmi ya fiddasu kunya kan lamarin tsaro a yankin.
Shugaban gamayyar, Injiniya Zanna Goni da shugaban mata, Hajia Mairo Bichi, ne suka rattafa hannu kan jawabin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Saboda haka, dattawan sun yi kira ga sauran shugabannin Arewa su sanya baki kan fadin gaskiyar abinda ke faruwa a yanzu domin janyo hankalin hukumomi.
Musamman, sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a lamarin tsaron kasar nan, domin samun sakamako mai kyau. Jawabin yace: “Muna masu yabawa Sultan na Sokoto, mahaifinmu, kan fayyace gaskiyan abubuwan da ke faruwa a Arewa, kan tsaro.”
“Muna kara jaddadawa, lamarin tsaro yayi munin da manomanmu ba sa iya zuwa gonakinsu, har matafiya ba sa iya tafiya cikin kwanciyar hankali saboda tsoron masu garkuwa.”