CBN ta ki Amincewa da Cire Rubutun Larabcin Dake Jikin Naira

Lauyan ya shigar da kara kotu domin bukatar cire rubutun ajami daga kan Naira.

Ya ce ana kokarin Musuluntar da Najeriya kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya Babban bankin Najeriya CBN ta nuna rashin amincewarta da karar da wani ya shigar babban kotun tarayya dake Legas na bukatar cire rubutun larabcin dake kan takardar kudin Najeriya ‘Naira’.

Wani Lauya mazauni jihar Legas, Malcom Omirhobo, wanda ya shigar da kara gaban Alkali Mohammed Liman, ya ce rubutun yaren larabcin dake jikin Naira na nuna cewa Najeriya kasar Musulunci ce alhalin ba haka take a kundin tsarin mulki ba.

Lauyan, wanda yace shi bai san ma’anar rubutun ajamin ba, ya bukaci kotu ta cire kuma ta maye gurbin da na Turanci, ko kuma harsuna uku mafi shahara a Najeriya watau Hausa, Yoruba ko Igbo.

A cewar lauyan, da rubutun ajamin, CBN ta saba sashe 10 da 55 na kundin tsarin mulkin Najeriya, PUNCH ta ruwaito.

Amma a cewar lauyan CBN, yace “rubutun ajamin dake kan kudin Najeriya ba ya nufin wani addini ko hulda da larabawa.”

Lauyan CBN ya caccaki lauyan kan ikirarin cewa rubutun ajamin barazana ce ga yancin addini a Najeriya.

“Rubutun dake kan takardar kudin kasar nan ba barazana bane ga kasa kuma bai sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ba.”

“Tun shekarar 1973 da aka canza kudin Najeriya daga Fam zuwa Naira ake amfani da rubutun Ajami.”

“Rubutun Ajami ba alama bane na Musulunci, innama an yi ne domin saukakawa wadanda basu iya karatun Boko ba wajen kasuwanci,” CBN tayi bayani.

CBN ya ce Najeriya za tayi asaran makudan kudi idan aka cire rubutun saboda za’a zubar da kudaden aka riga aka wallafa.

Alkali Liman Mohammed zai saurari karan ranar Talata (Yau) Hakazalika zai sake sauraron karar da wannan lauya dai ya shiga na cire rubutun larabcin dake jikin tambarin hukumar Sojin Najeriya.

Kamar CBN, hukumar Soji ta bukaci Alkalin yayi watsi da karar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here