Shugaban Chadi ya Sanya Hannu Kan Dokar Ta-ɓaci Kan Matsalar Abinci da ƙasar ke Fuskanta

Shugaban Chadi mai riƙon ƙwarya, Mahamat Idriss Deby, ya sanya hannu kan dokar ta-ɓaci kan matsalar abinci.

Ya ce ya kafa wannan doka ce saboda matsalolin ƙarancin abinci da ƙasar ke fuskanta a wannan shekara da kuma ƙaruwar al’umma da matsalolin jin-ƙai.

Shugaban ya kuma nemi taimako gabanni ganawa da shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Macky Sall da Vladimir Putin na Rasha kan abinci da ake shigarwa Chadi.

Majalisar Dinkin Duniya ta gargaɗi cewa al’ummar Chadi miliyan 5.5 – kashi 1 cikin 3 na al’ummar ƙasar – za su bukaci taimakon agaji a shekara mai zuwa.

Hukumar abinci ta duniya a watan Maris ta ce akwai ‘yan ƙasar sama da miliyan biyu da ke cikin matsananciyar yunwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here