Za’a Samar da Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa (ECC) Akalla ɗaya a Kowace Jaha – Dr Pantami
Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr Isa Pantami, yace za’a samar da cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) akalla ɗaya a kowace jaha.
Ministan yace a halin yanzun ma’aikatarsa ta ƙaddamar da ECC 23 a faɗin ƙasar nan kuma akwai sauran 13 dake tafe.
Yace ECC zata taimaka wa yan Najeriya wajen isar da sako cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da an caje su kuɗi ba.
Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami, ya bayyana shirinsa na samar da aƙalla cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) ɗaya a kowace jaha kafin ƙarewar 2022, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
Ministan ya faɗi haka ne a wajen ƙaddamar da sabon tsarin tattalin arziƙin zamani rukuni na 10 a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar Pantami, an ƙaddamar da ECC 23 a faɗin Najeriya, kuma akwai ragowar 13 da ake cikin aikin su.
Rahoton BBC ya nuna cewa tuni ministan ya buɗe ofishin farko a wannan tsarin a jihar Katsina matakin da ya bai wa sama da mutum 40 aikin yi.
Yace: “A cikin shekaru biyu, mun buɗe sabbin Cibiyoyin amsa kiran gaggawa 23 a faɗin Najeriya, kuma kawai sauran 13 dake tafe.”
“Tsarin da muka yi shine a samar da aƙalla ECC ɗaya a kowacce jaha dake faɗin Najeriya kafin ƙarshen shekarar 2022.”
“Waɗannan cibiyoyin suna da matuƙar amfani, Lamba ce da zakai amfani ita kyauta, idan ka kira lambar ba za’a caje ka ko sisi ba.”
Pantami ya kara da cewa wannan tsarin zai taimaka wa yan Najeriya wajen bada haɗin kai da taimaka musu wajen isar da saƙon gaggawa musamman akan tsaro.
a