Cigaba Guda Tare(9) da Ministan Sadarwa ya Kawo Najeriya a 2020

 

Kamar yadda kuka sani, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Isah Ali Ibrahim Pantami a matsayin ministan sadarwa da tattali arzikin zamani na Najeriya.

Sai dai an samu gagarumin ci gaba a bangaren fasahar sadarwa cikin dan kankanin lokaci da hawarsa kujerar.

Wadannan nasarori da aka samu sun samune bayan kaddamar da tsarin manyan ayyuka na habbaka tattalin arzikin zamani na Najeriya tare da magance wasu manyan matsaloli da suke kawo cikas fiye da qarni guda da ya wuce a bangaren sadarwa.

A wannan zaure, Legit.ng ta kawo maku jerin wasu manyan ayyuka 9 da ma’aikatar Pantami ta gudanar a shekarar 2020.

1. A ranar 22 ga watan Janairun 2020, an kulla yarjejeniya da kamfanin IBM domin ba yan Najeriya damar cin moriyar fasahar zamani daga gidajensu.

2. Ministan sadarwa, Dr Pantami ya zanta da kungiyar gwamnonin Najeriya sannan ya magance matsalolin Right of Way (ROW) a Najeriya.

Wannan matsala ta ROW dai ita ce rashin damar da kamfanonin sadarwa suke samu wajen kafa karafunan kamfanoninsu a filayen da mutane suka mallaka, wanda yake matukar haifar da cikas wajen fadada harkokin sadarwa a Nigeria.

3. Ministan ya gabatar da jawabin yaye dalibai a jami’ar fasaha ta tarayya da ke Minna sannan ya kuma wakilci shugaba Buhari a bikin yaye daliban a ranar 31 ga watan Janairun 2020.

4. A ranar 20 ga watan Yunin 2020, an kammala tare da kaddamar da Cibiyar koyon fasahar sadarwa ta Arewa maso Yamma da aka gina a jihar Jigawa.

5. A ranar 17 ga watan Fabreru 2020, ma’aikatar sadarwa ta ƙaddamar da shirin bai wa ɗaliban Sakandire horo kan yadda za su bunkasa ilimin sadarwa a zamanance.

6. A ranar 9 ga watan Maris, ma’aikatar sadarwa ta ƙasa ta samu nasarar rufe layukan miliyan biyu da dubu ɗari biyu (2,200,000) waɗan da ba ‘a yi wa rejista ba.

Domin daƙile yaɗuwar masu aikata laifukan ta’addanci, da kuma taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da bincike

7. Shugaba Buhari ya kaddamar tsarin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa na zamani wanda zaiyi aikin fadada karfin hanyoyin sadarwa da ake dashi a cikin kasa don a karfafa tattalin arzikin zamani sannan a koyar da ‘yan Najeriya ilmin fasaha.

8. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin National Broadband Plan na shekarar 2020 zuwa 2025, sannan ya kaddamar da ginin babban dakin taro na ma’aikatar sadarwa.

Ya ƙaddamar da 112 a matsayin lambar kiran gaggawa ta ƙasa, kuma ba za a caji ko kwabo a kiran ba.

9. Ilimin kasuwanci na zamani: Minista Pantami ya ƙaddamar da kwamitin shawara na shirin MIT a ranar 26 ga watan Maris, 2020.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here