An Cigaba da Harbe-Harben Bindiga a Gidan Gyaran Hali Dake Jos

Rahotanni sun bayyana cewa an jiyo karar harbe-harben bindiga a gidan gyaran hali dake Jos, babban birnin Filato ranar Lahadi .

Jami’in yaɗa labarai na rundunar sojin Operation Safe Haven, Mejo Ishaku, yace yanzun haka jami’an rundunarsu sun kai ɗauki.

Ana tsammanin wasu tsagerun yan bindiga ne suke kokarin fasa gidan yarin amma jami’an tsaro sun tarbe su.

Jos, plateau – Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa yanzu haka ana cigaba da jin karar harbe-harbe a gidan gyaran halin Jos, jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa karar harbe-harben ya fara tashi ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi.

A halin yanzun jami’an tsaro sun mamaye baki ɗaya ilahirin yankin, inada suke cigaba da kula da zirga-zirgan mutane a yankin.

Jami’an tsaro sun kai ɗauki Rahoton channels tv ya nuna cewa wasu tsagerun yan bindiga ne ke kokarin kutsa kai gidan yarin, amma jami’an tsaro sun tarbe su ana musayar wuta.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar sojin Opertion Safe Haven, Mejo Ishaku, ya tabbatar da lamarin, yace har yanzun ba’a gano su waye suka farmaki gidan yarin ba.

Ishaku ya kara da cewa jami’an rundunarsa na can yanzun hakasuna fafatawa da maharan domin dakile yunkurin su.

Wannan gidan gyaran hali da ake kokarin fasawa yana tsakiyar Jos, babban birnin Filato, kuma yan kusa da hedkwatar yan sandan jihar.

Yanzun haka an tsammanin jami’an yan sanda na Division A zasu kawo ɗauki domin dakile harun, kasancewa ofishin su na kusa da wurin.

Cikakken bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here